ABNA24 : Kiyanoush ya kara da cewa; Kamfanin da ya samar da riga-kafin ya sami izini daga hukumar abinci da magani ta kasa, kuma mutanen da aka yi wa riga-kafin na farko ana bibiyar halin da suke ciki na tsawon wata daya.
Kakakin hukumar abinci da magani na Iran din ya kuma bayyana cewa; Mutanen da aka yi gwajin na farko shekarunsu suna tsakanin shekaru 18 zuwa 50, kuma wadanda ba su dauke da wasu cutuka ne masu rikitarwa ko cutar corona.
342/